Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar Najeriya bata samu muhimmin gudunmuwa daga tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ba, musamman game da yaki da rikciin ta’addanci na Boko Haram, inji rahoton Premium Times.
Kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, ga watan Afrilu, a babban birnin kasar Amurka, Washington DC, a wata tattaunawa da yayi da yan jaridu, inda ya kara da cewa dangantakar Amurka da Najeriya ta karfafa tun bayan darewar shugaban kasar, Donal Trump.
Ana sa ran Buhari da Trump zasu gana da ranar Litinin, 30 ga watan Afrilu, inda tattaunawarsu zata ta’alakka ne kacokan kan matsalar tsaro, musamman ta’addanci da ya yawaita a Duniya, da kuma hanyoyin shawo kan matsalar.
Obama da Buhari
Garba shehu yace: “Buhari ne shugaba a yankin Afirka na bakar fata na farko daya gana da Trump a fadar White House, hakan na nufin martabar Najeriya ta karu kenan a idon Duniya, shuwagabannin zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
“idan zaku tuna shugaba Buhari ya taba yin korafi a bayyana cewa Najeriya bata samun cikakken goyon baya daga gwamnatin Obama a kokarin da take yin a yaki da kungiyar ta’addan na Boko Haram, amma tun bayan kaucewar gwamnatin Obama, shugaba Trump na bada hadin kai.” Inji shi
JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL
GET MOVIE UPDATES ON WHATSAPP
Download Complete Korean series with English subtitle, Download Full Indian movie with English subtitle, FZ movies download, Netnaija movies download, O2tvseries
We tell you where to download and how to download your favorite movies